1. Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,
2. cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.
3. Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!
4. Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.