5. Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.
6. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7. To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra'ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.
8. Yadda yake a rubuce cewa,“Allah ya toshe musu basira,Ya ba su ido, ba na gani ba,Da kuma kunne, ba na ji ba,Har ya zuwa yau.”
9. Dawuda kuma ya ce,“Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu,Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.
10. Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani,Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”
11. Ina kuma tambaya. Faɗuwar da suka yi, sun faɗi ba tashi ke nan? A'a, ko kusa! Sai ma faɗuwarsu ta zama sanadin ceto ga al'ummai, don a sa Isra'ila kishi.
12. To, in kuwa duniya ta arzuta da hasararsu, wa zai kimanta yawan albarka, in adadinsu masu ɗungumawa ga Allah ya cika?
13. Da ku al'ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al'ummai, ina taƙama da aikina,
14. ko ta wane hali in sa kabilata kishin zuci, har in ceci waɗansunsu.
15. Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba?
16. In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.
17. Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
18. kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai.
19. Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.”