Oba 1:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Waɗanda kake amana da su,Za su kore ka daga ƙasarka.Mutanen da suke amana da kai,Za su yaudare ka,Su ci ka da yaƙi.Abokan nan naka da kake ci tare dasu za su kafa maka tarko,Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayonnan nasa?’ ”

8. Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.

9. Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.

10. “Saboda kama-karyar da ka yi waYakubu ɗan'uwanka,Za a sa ka ka sha kunya,Za a hallaka ka har abada.

Oba 1