5. Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama'a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki.
6. Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu.
7. Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seraiya, da Re'elaya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba'ana.
46-56. Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.
57-59. Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.
60. Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
61-62. Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu.
63. Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.
64. Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.