19. Sai na ce wa manya da shugabanni, da sauran jama'a, “Aikin nan babba ne, mai yawa kuma, ga shikuwa, muna rarrabe a kan garun nesa da juna.
20. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu.”
21. Haka kuwa muka yi aikin, rabinmu na riƙe da māsu tun daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.
22. A wannan lokaci kuma na ce wa jama'a, kowane mutum tare da baransa ya kwana a Urushalima domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.
23. Saboda haka ni, da 'yan'uwana, da barorina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa. Kowa yana riƙe da makami.