8. Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.
9. Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa'an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.
10. Na kuma iske ba a ba Lawiyawa rabonsu ba. Saboda wannan Lawiyawa da mawaƙa masu hidima suka watse zuwa gonakinsu.
11. Sai na yi wa shugabanni faɗa, na ce, “Me ya sa aka ƙi kula da Haikalin Allah?” Sa'an nan na tara Lawiyawa da mawaƙa, na sa su a wuraren aikinsu.