15. Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni,
16. da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah.
17. Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.
18. Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.
19. Masu tsaron ƙofofi kuma su ne Akkub, da Talmon, da 'yan'uwansu, su ɗari da saba'in da biyu ne.
20. Sauran jama'ar Isra'ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa.
21. Amma ma'aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma'aikatan Haikali.