16. Kin yawaita 'yan kasuwanki suna dayawa fiye da taurari,Amma sun tafi kamar fara waɗandasukan buɗe fikafikansu su tashi, sutafi.
17. Shugabanninki kamar ɗango suke,Manyan mutanenki kamarcincirindon fāra ne,Suna zaune a kan shinge a kwanakinsanyi,Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi sutafi,Ba wanda ya san inda suke.
18. Ya Sarkin Assuriya, masu tsaronkasuna barci,Manyan mutanenka sunakwankwance,Mutanenka sun watse cikinduwatsu,Ba wanda zai tattaro su.
19. Ba abin da zai rage zafin rauninka,Rauninka ba ya warkuwa.Duk wanda ya ji labarinka, zai tafahannuwansaGama wane ne ba ka musguna waba?