Mika 6:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ku duwatsu da madawwaman tussanduniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yimuku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.

3. “Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!

4. Gama na fito da ku daga ƙasarMasar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.

5. Ya ku jama'ata, ku tunaDa abin da Balak, Sarkin Mowab, yaƙulla,Da yadda Bal'amu ɗan Beyor yaamsa masa,Da abin da ya faru daga Shittim, harzuwa Gilgal,Don ku san ayyukan adalci naUbangiji.”

Mika 6