Mika 2:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Kukan kori matan mutanenaDaga gidajensu masu kyau,Kukan kawar da darajata har abadadaga wurin 'ya'yansu.

10. Ku tashi, ku tafi,Gama nan ba wurin hutawa ba ne,Saboda ƙazantarku wadda take kawomuguwar hallaka.

11. “Idan mutum ya tashi yana iskanci,yana faɗar ƙarya, ya ce,‘Zan yi muku wa'azi game da ruwaninabi da abin sa maye,’To, shi ne zai zama mai wa'azinmutanen nan!

Mika 2