Mat 6:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,

4. domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

5. “In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.

6. Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.

7. “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.

8. Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

Mat 6