2. Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.
3. Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.
4. Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu.
5. Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.
6. Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.
7. Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.”