Mat 25:28-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.

29. Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

30. Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

Mat 25