30. Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.
31. To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.
32. Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
33. “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.
34. Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.
35. Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.
36. Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.
37. Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’
38. Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’
39. Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.
40. To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”
41. Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42. Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,‘Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.Wannan aikin Ubangiji ne,A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’
43. Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.
44. Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”