Mat 15:24-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”

25. Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”

26. Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”

27. Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”

Mat 15