Mat 14:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”

9. Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.

10. Ya aika aka fille wa Yahaya kai a kurkuku,

11. aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwa tasa.

12. Almajiransa suka zo suka ɗauki gangar jikin, suka binne, suka kuma je suka gaya wa Yesu.

13. Da Yesu ya ji haka sai ya tashi daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, domin ya kaɗaita. Amma da taron jama'a suka ji haka, suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.

14. Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.

Mat 14