21. Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.
22. Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.
23. Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”
24. Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.