28. Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.
29. Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.
30. Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”