29. Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba.
30. Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.
31. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
32. “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.
33. Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”
34. “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.