17. Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu.
18. Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.
19. A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin.
20. Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.
21. 'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.
22. Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
23. In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.