2. Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!
3. Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.
4. Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin 'yan'uwansa, da kuma gidansu.”
5. Bai ko iya yin wata mu'ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su.
6. Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7. Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
8. Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,
9. amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.
10. Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.
11. Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”
12. Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.
13. Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.
14. Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
15. Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”
16. Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yahaya, wanda na fille wa kai, shi ne aka tasa.”
17. Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.
18. Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan'uwanka ba.”
19. Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,