9. Na ga wannan duka a sa'ad da nake tunani a kan abubuwan da ake yi a duniyan nan, duniyar da waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.
10. Hakika na ga an kai mugaye an binne, amma a birnin nan inda suka aikata wannan mugun abu, mutane suna yabonsu, amma sun kuma manta da su. Wannan kuma aikin banza ne.
11. Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.
12. Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai.
13. Ga mugaye ba zai tafi daidai ba, kamar inuwa ransu yake. Za su yi mutuwar ƙuruciya domin ba su da tsoron Allah.