M. Had 10:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.

12. Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi.

13. Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka.

14. Wawa ya cika yawan surutu.Wa ya san abin da zai faru nan gaba? Wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

M. Had 10