Luk 6:25-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. “Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.

26. “Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

27. “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.

Luk 6