11. Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.
12. A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah.
13. Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni.
14. Su ne Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas,
15. da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,
16. da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.