50. Sai ya kai su waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
51. Yana sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka ɗauke shi zuwa sama.
52. Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima, suna matuƙar farin ciki.
53. Ko yaushe kuma suna a Haikali suna yabon Allah.