Luk 22:68-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

68. In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba.

69. Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”

70. Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”

71. Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”

Luk 22