41. Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,
42. ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku.
43. Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,
44. su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”
45. Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa,
46. ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.’ Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”