26. ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa.
27. Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”
28. Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima.
29. Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,
30. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.
31. Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ”
32. Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu.
33. Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”
34. Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.”
35. Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.
36. Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya.
37. Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.
38. Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”
39. Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajiranka mana!”
40. Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”
41. Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,
42. ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku.
43. Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,
44. su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”
45. Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa,