Luk 10:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.

2. Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi.

3. To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai.

Luk 10