L. Mah 13:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu,

5. gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.”

6. Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala'ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba.

L. Mah 13