23. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
24. “Wannan ita ce ka'idar aikin Lawiyawa, tun daga mai shekara ashirin da biyar zuwa gaba, zai shiga yin aiki a alfarwa ta sujada.
25. Amma daga shekara hamsin, sai su huta daga aiki alfarwa ta sujada.
26. Amma su taimaki 'yan'uwansu da tafiyar da ayyuka a cikin alfarwa ta sujada, sai dai ba za su ɗauki nauyin gudanar da aikin ba. Haka za ka shirya wa Lawiyawa aikinsu.”