L. Kid 6:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.

5. A dukan kwanakin wa'adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.

6. A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.

7. Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan'uwansa, ko ta 'yar'uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.

8. Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.

9. Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai.

10. A rana ta takwas kuwa zai kawo wa firist 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a bakin ƙofar alfarwa ta sujada.

L. Kid 6