15. Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu.Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.
16. Ele'azara kuwa, ɗan Haruna, firist, shi ne zai lura da man fitila, da turare, da hadayar gari ta kullum, da man keɓewa, ya kuma kula da dukan alfarwar, da duk abin da yake cikinta, da Wuri Mai Tsarki, da kayayyakinsa.
17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
18. “Kada ku bar zuriyar Kohat
19. ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da 'ya'yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka.
20. Amma idan Kohatawa suka shiga alfarwar suka tarar firistoci suna shisshirya tsarkakakkun abubuwa don tashi, har dai in sun gani, to za su mutu.”
21. Ubangiji ya kuma faɗa wa Musa,
22. ya ƙidaya 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu
23. ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.