L. Kid 34:15-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”

16. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

17. “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.

18. Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar.

19. Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.

20. Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu.

21. Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu.

22. Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan.

23. Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa,

24. da Kemuwel ɗan Shiftan daga kabilar Ifraimu.

25. Elizafan ɗan Farnak daga kabilar Zabaluna.

26. Faltiyel ɗan Azzan daga kabilar Issaka.

27. Ahihud ɗan Shelomi daga kabilar Ashiru.

28. Fedahel ɗan Ammihud daga kabilar Naftali.”

29. Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba wa jama'ar Isra'ila gādon ƙasar Kan'ana.

L. Kid 34