5. Isra'ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot.
6. Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin.
7. Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba'al-zefon suka sauka a gaban Migdol.
8. Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara.
9. Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can.
10. Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.
11. Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.
12. Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.
13. Daga Dofka suka tafi Alush.
14. Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.
15. Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.