8. Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.
9. Isra'ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.
10. Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.
11. Da mutum da dabba sun kwashe su ganima.
12. Suka kawo bayin da ganimar a wurin Musa, da Ele'azara firist, da taron jama'ar Isra'ila a zango a filayen Mowab a Kogin Urdun daura da Yariko.
13. Sai Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar Isra'ila suka fita zango su tarye su.
14. Musa kuwa ya husata da shugabannin sojoji waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga wurin yaƙi.
15. Ya tambaye su ya ce, “Don me kuka bar dukan mata da rai?
16. Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji.
17. Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.
18. Amma dukan 'yan mata da ba su san maza ba, sai ku bar wa kanku.