11. idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata.
12. Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa'adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.
13. Mijinta yana da iko ya tabbatar, ko kuwa ya rushe kowane wa'adi da kowane irin alkawarin da ta ɗauka.
14. Idan mijinta ya yi shiru, bai ce mata kome ba, to, dole ta cika kowane abu da ta yi wa'adi da wanda kuma ta ɗauki alkawarinsa. Shirun da ya yi ya yardar mata.
15. Amma idan ya ji, sa'an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukunci a maimakon matar.