L. Kid 27:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra'ilawa.

13. Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi,

14. domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)

15. Musa kuwa ya ce wa Ubangiji,

16. “Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan 'yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama'ar,

17. mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”

18. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka,

19. ka sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron, sa'an nan ka keɓe shi a gabansu.

20. Ka danƙa masa ikonka don taron jama'ar Isra'ila su yi masa biyayya.

L. Kid 27