L. Kid 24:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ina ganinsa, amma ba yanzu ba,Ina hangensa, amma ba kusa ba.Tauraro zai fito daga cikin Yakubu,Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila,Zai ragargaje goshin Mowabawa,Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.

18. Za a mallaki Edom,Hakka kuma za a mallaki Seyir abokiyar gābanta,Isra'ila za ta gwada ƙarfi.

19. Yakubu zai yi mulki,Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”

20. Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Amalek na fari ne cikin al'ummai,amm ƙarshensa hallaka ne.”

21. Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Wurin zamanku mai ƙarƙo ne,Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.

22. Duk da haka za a lalatar da Keniyawa.Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?”

L. Kid 24