L. Kid 23:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.

4. Da Ubangiji ya sadu da Bal'amu, sai Bal'amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.”

5. Ubangiji kuwa ya sa magana a bakin Bal'amu ya ce, “Koma wurin Balak, ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”

6. Sai ya koma wurin Balak, ya same shi da dukan dattawan Mowab suna tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa.

7. Bal'amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce“Tun daga Aram Balak ya kawo ni,Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu.‘Zo, la'anta mini Yakubu,Zo, ka tsine wa Isra'ila!’

8. Ƙaƙa zan iya la'anta wanda Allah bai la'antar ba?Ƙaƙa zan iya tsine wa wanda Ubangiji bai tsine wa ba?

9. Gama daga kan duwatsu na gan su,Daga bisa kan tuddai na hange su,Jama'a ce wadda take zaune ita kaɗai,Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al'ummai.

L. Kid 23