16. Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.
17. Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.”
18. Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.”
19. Amma mutanen Isra'ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”
20. Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su.