L. Kid 2:18-24-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Duk sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Zangon zai kasance a kewaye da alfarwa ta sujada.

3-9. Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka,(186,400) dubu ɗari da tamanin da shida da ɗari huɗu.Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya.

18-24. Ƙungiyoyin kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabilar Shugaba Jimilla Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500 Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200 Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400 Jimilla duka, (108,100) dubu ɗari da takwas, da ɗari ɗaya daidai.Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin.

25-31. Ƙungiyoyin kabilar Dan za su sauka su kafa tutarsu a sashin arewa a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai 62,700 Ashiru Fagiyel ɗan Okran 41,500 Naftali Ahira ɗan Enan 53,400 Jimilla duka, (157,600) duba ɗari da hamsin da bakwai, da ɗari shida.Ƙungiyoyin Dan za su bi daga bayan duka.

32. Jimillar yawan Isra'ilawa da aka rubuta su a yadda suke ƙungiya ƙungiya, su dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin ne (603,550).

33. Amma kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ba a rubuta Lawiyawa haɗe da sauran Isra'ilawa ba.

34. Saboda haka Isra'ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.

L. Kid 2