L. Kid 2:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan umarnai.

2. Duk sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Zangon zai kasance a kewaye da alfarwa ta sujada.

10-16. Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su sauka su kafa tutarsu a sashin kudu a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur 46,500 Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai 59,300 Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel 45,650 Jimilla duka, 151,450) duba ɗari da hamsin da ɗaya, da ɗari huɗu da hamsin.Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su bi bayan na Yahuza.

18-24. Ƙungiyoyin kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabilar Shugaba Jimilla Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500 Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200 Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400 Jimilla duka, (108,100) dubu ɗari da takwas, da ɗari ɗaya daidai.Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin.

L. Kid 2