L. Kid 14:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?”

4. Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.”

5. Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa.

L. Kid 14