8. Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”
9. Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su.
10. Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.
11. Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta.