11. Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta.
12. Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.”
13. Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”
14. Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.”
15. Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.
16. Bayan wannan jama'a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.