L. Kid 11:4-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra'ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?

5. Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.

6. Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”

7. Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.

8. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.

9. Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.

10. Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.

11. Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?

12. Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’

13. A ina zan samo nama da zan ba wannan jama'a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’

14. Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina.

15. Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.”

16. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.

17. Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.

18. Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.

19. Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba.

20. Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa , suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”

21. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur.

22. Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?”

L. Kid 11