L. Kid 1:3-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

4. Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”

5-15. Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa. Kabila Shugaban Kabila Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Naftali Ahira ɗan Enan

16. Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki.

17. Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu,

18. suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,

19. kamar yadda Ubangiji ya umarta.Musa ya rubuta jama'a a jeji ta Sinai.

47. Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba,

48. gama Ubangiji ya ce wa Musa,

49. “Sa'ad da kake ƙidaya Isra'ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi.

50. A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita.

51. Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi.

52. Sauran Isra'ilawa za su sauka ƙungiya ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa a ƙarƙashin tutarsa.

53. Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.”

54. Sai Isra'ilawa suka aikata kowane abu da Ubangiji ya umarci Musa.

L. Kid 1