L. Kid 1:1-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,

2. “Da kai da Haruna ku ƙidaya Isra'ilawa, bisa ga kabilansu da iyalansu. Ku tsara sunayen dukan mazaje

3. daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

4. Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”

16. Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki.

17. Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu,

18. suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,

19. kamar yadda Ubangiji ya umarta.Musa ya rubuta jama'a a jeji ta Sinai.

L. Kid 1